Allah ya amince da gwamnatinka – Okorocha ga Buhari

Allah ya amince da gwamnatinka – Okorocha ga Buhari

Shugaban gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya yabama Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan abunda ya bayyana a matsayin kokari wajen hada kan kasa.

A cewar gwamnan na jihar Imo an cimma hadin kan kasar ne ta hanyar shugabancin Buhari.

Ya kara da cewa nasarorin Buhari tabbaci ne ga cewar Allah ya amince da gwamnatinsa, inda yace yan Najeriya sunyi farin ciki matuka da shi.

Allah ya amince da gwamnatinka – Okorocha ga Buhari

Allah ya amince da gwamnatinka – Okorocha ga Buhari

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron cin abinci da gwamnonin suka yi tare shugaban kasar a Daura.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta yayi magana akan sauya shekar manyan yan siyasa daga jam’iyya daya zuwa wata.

KU KARANTA KUMA: Buratai ya ziyarci sojojin dake kwance a asibiti a Maiduguri

Shugaban kasar yayiwa masu sauya sheka fatan alkhairi. “Ga wadanda suka yanke shawarar chanja jam’iyyu saboda wasu dalilai,muna yi masu fatan alkhairi,” inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel