Buratai ya ziyarci sojojin dake kwance a asibiti a Maiduguri

Buratai ya ziyarci sojojin dake kwance a asibiti a Maiduguri

Babban hafasan sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya ziyarci sojojin Najeriya dake kwance a asibiti suna jinya a asibitin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Buratai ya bayyanawa sojojin da suka sami rauni sakamakon yaki da yan ta’addan Boko Haram cewa sadaukar da jikin da rayukan su da suka yi ba zai tafi a banza ba.

Bayan yi musu addu’ar Allah ya basu lafiya, ya ce za a wadata su da dukkanin magungunan da suke bukata domin samun lafiya cikin gaggawa.

Buratai ya ziyarci sojojin dake kwance a asibiti a Maiduguri

Buratai ya ziyarci sojojin dake kwance a asibiti a Maiduguri

Shugaban asibitin Samuel Adama ya jinjinawa Buratai kan wannan ziyara da yayi wa sojojin da ke kwance a asibitin.

Sannan kuma da yin amfani da wannan dama don yi musu barka da Sallah.

KU KARANTA KUMA: 2019: Buhari yayiwa Saraki, Akpabio da sauran wadanda suka sauya sheka fatan alkhairi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Al’umman yankin Ikorodu dake jihar Lagas sun wayi gari cikin fargaba yayinda fusatattun sojoji suka kaiwa yankin kawanya.

Mamayar ya kasance harin daukar fansa, sakamakon kisan wani soja da ake zargin yan kungiyar asiri da aikatawa a yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel