Kishin-Kishin: Baraka ta fara kunno kai a tsakanin Buba Galadima da Kwankwaso

Kishin-Kishin: Baraka ta fara kunno kai a tsakanin Buba Galadima da Kwankwaso

- Baraka ta kunno kai tsakanin Buba Galadima da Kwankwaso

- A da dai mutanen biyu aminan juna ne

- Har yanzu Buba Galadima bai koma PDP ba

Wasu labaran da ke samun mu na tabbatar mana da cewa tuni baraka ta soma kunno kai a tsakanin fitaccen dan adawar nan kuma tsohon aminin shugaba Buhari watau Buba Galadima da kuma Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Kishin-Kishin: Baraka ta fara kunno kai a tsakanin Buba Galadima da Kwankwaso

Kishin-Kishin: Baraka ta fara kunno kai a tsakanin Buba Galadima da Kwankwaso
Source: Getty Images

KU KARANTA: PDP ta gwalashe Kwankwaso

Majiyar mu dai ta bayyana mana cewa tun kafin zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a shekarar 2015 mutanen biyu suka kulla amintaka inda shi Buba Galadima din ya goyi bayan Kwankwaso a maimakon Buhari amma a 'yan kwanakin nan an rabu da ganin su a tare.

Legit.ng ta samu cewa shugaban jam'iyyar na APC bangaren 'yan aware, watau Buba Galadima har yanzu dai bai fice daga jam'iyyar ba kamar yadda uban gidan nasa ya yi a kwanakin baya.

Haka zalika wasu dake kusa da Buba Galadima din suna cewa Buba Galadiman ya fasa fita daga jam'iyyar inda aka ruwaito cewa tuni ya fara kamun kafa domin a maida shi jam'iyyar ta APC kuma su cigaba da tarayyar su da Buhari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel