Anzo Wajen: Tsohon gwamnan Delta Udaughan zai koma APC

Anzo Wajen: Tsohon gwamnan Delta Udaughan zai koma APC

- Dr. Emmanuel Udaughan ya shirya ficewa daga jam'iyar PDP zuwa APC

- Ya ce bai kamata ace jihar Delta na a bangaren masu adawa ba

- Ana sa ran Udaughan zai sayi tikitin tsayawa takarar sanata a Delta ta kudu karkashin APC

Tsohon gwamnan jihar Delta, Dr. Emmanuel Udaughan, ya fito fili ya bayyana kudirinsa na barin jam'iyar adawa ta PDP zuwa jam'iya mai mulki ta APC, bayan da ya samu matsin lamba daga jama'arsa na sauya shekar.

Sai dai yace sauya shekar bata da alaka da shugaban jam'iayar ta APC Adams Oshiomhole.

"Dalilin da ya sa zan sauya wannan sheka ya shafi halin da PDP take ciki a yanzu, da kuma tunanin makomar siyasata a nan gaba. Haka zalika nayi duba ga irin salon da siyasar kasar take ciki a yanzu, da kuma makomar magoya bayana.

"Na yi kyakkyawan karatun tanustu akan siyasar kasarnan, da hakan na yanke hukuncin cewa bai kamata juhar Delta ta kasance a bangaren masu adawa ba" a cewar sa.

KARANTA WANNAN: Hajjin bana: An kama wani dan arewacin Najeriya a Saudiyya saboda dukan dan sanda

Da aka tambaye shi ko sun tattauna da Comrade Oshiomhole dangane da wannan sauya sheka tasa, Uduagban ya ce: "Eh kwarai mun tattauna hakan, muna tattaunawa kamar yadda muka saba a baya, amma ku sani ba wai tursasawa ba ce, shi kansa ya so in shiga jam'iyar.

"Sai dai tun a lokutan baya,na sanar da shi cewa ina da iyayen gida a wannan siyasar da nike ciki, akwai Chief James Onanefe Ibori, ya kamata ace sun tattauna".

Bayanan da Legit.ng ta tattara ya nuna cewa tsohon gwamnan zai yi rijistar zama cikakken dan jam'iyar APC, tare da yankar tikitin tsayawa takarar sanata mai wakiltar mazabar Delta ta kudu a majalisar dattijai ta jihar.

Haka zakika ana sa ran zaiyi aiki kafada-da-kafada da sauran shuwagabannin jam'iyar a jihar, da suka hada da Chief Great Ogboru, wanda ya kayar da shi a zaben gwamnan jihar shekara uku da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel