2019: Buhari yayiwa Saraki, Akpabio da sauran wadanda suka sauya sheka fatan alkhairi

2019: Buhari yayiwa Saraki, Akpabio da sauran wadanda suka sauya sheka fatan alkhairi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta yayi magana akan sauya shekar manyan yan siyasa daga jam’iyya daya zuwa wata.

A wajen wani taron cin abinci tare da wasu gwamnonin APC inda suka samu rakiyar wasu mambobin majalisunkasa a na jihad a kuma kwamishinoni, shugaban kasar yayiwa masu sauya sheka fatan alkhairi.

“Ga wadanda suka yanke shawarar chanja jam’iyyu saboda wasu dalilai,muna yi masu fatan alkhairi,” inji shi.

Yan watannin da suka gabata, yan majalisa da dama tare da mabiyansu sun sauya sheka domin shiryawa zabukan 2019.

2019: Buhari yayiwa Saraki, Akpabio da sauran wadanda suka sauya sheka fatan alkhairi

2019: Buhari yayiwa Saraki, Akpabio da sauran wadanda suka sauya sheka fatan alkhairi

Daga cikin wadanda suka sauya shekar sun hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, Gwamna Abdulfatah Ahmed na Kwara da tsohon Gwamna Godswill Akpabio na Akwa Ibom. Yayinda mutane ukun farko suka bar APC zuwa PDP, Mista Akpabio, ya bar PDP ne zuwa APC.

KU KARANTA KUMA: Kada ku bari 'yan siyasa su yi amfani da ku - Sarkin Musulmi ga matasa

Yayinda Akpabio ya sauka daga matsayinsa na shugaban marasa rinjaye a majalisa, Saraki yaki sauka daga nasa matsayin.

Sai dai shugaban kasa Buhari bai yi magana akan ko Saraki ya sauka ko kada ya sauka ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel