Za'a rataye bakwai saboda kissan mutum guda - Kotu

Za'a rataye bakwai saboda kissan mutum guda - Kotu

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wasu mutane bakwai da aka samu da laifin fashi da makami da kisan wani dan kasuwan mazaunin Amurka a shekarar 2017 yayin da yazo hutu a Akure.

Wata babban kotun jihar Ondo da ke zamanta a Akure ta zartas da hukuncin kisa a kan wasu mutane bakwai saboda kisar wani dan kasuwan mai suna Banji Adafin.

Dan kasuwan wanda ke zaune a Amurka ya gamu da ajalinsa ne a ranar 4 ga watan Yulin shekarar 2017 a gida mai lamba 5 Temidire Street yayin da yazo hutu a Akure.

Bayan kashe dan kasuwan an gano cewa wanda aka zartas wa da hukuncin sun sace kayayakin alatu daga gidan mamacin. Wasu daga cikin abubuwan da suka sace sun hada da talabijin, kwamfyuta, wayar salula, ipads da kudade da ba'a bayyana adadinsu ba.

Kotu ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane 7 saboda kisar wani dan kasuwa

Kotu ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane 7 saboda kisar wani dan kasuwa

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

An gurfanar da mutane bakwai din ne kan laifin hadin baki wajen aikata fashi da makami da kisa wanda ya ci karo da sashi 6(b) na dokar fashi da malakar bindiga na dokar Najeriya ta shekarar 2004.

Masu laifin da za'a zartar musu da hukuncin kisa ta hanyar rataya ko harbin bindiga sun hada da Jimoh Sadiq (Akamo), Blessing Ogunlade, Yomi Balogun (Regal), Akeem Adedayo, Oso John Omoniyi (Bosco) da Sadiq Babatunde.

Daya daga cikin wanda aka yankewa hukucin zaman gidan yari na shekara daya, Damilola Samuel (Mama) budurwar daya daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin kisa ne.

A lokacin da yake zartas da hukuncin, Alkalin kotun, Justice Ademola Bola ya ce bincike da gamsar da kotu cewa wadanda aka zartas wa hukuncin sun aikata laifin da ake tuhumarsu.

Alkalin kuma ya same su da laifin mallakar bindigogi ba kan ka'idda ba wanda laifi ne a karkashin sashi na 9 kuma hukucin laifin yana sashi na 2719(1) b na dokar mallakar bindigogi Cap F26 na Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel