Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta gwalashe Sanata Kwankwaso

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta gwalashe Sanata Kwankwaso

- Jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta gwalashe Sanata Kwankwaso

- Jam'iyyar ta ce ba zata kebance tikitin ta na takarar shugaban kasa ga Arewa maso yamma ba

- PDP tace tikitin takarar ta na shugaban kasa na dukkan wani dan Arewa ne

Yayin da zabukan gama gari na shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) ta babbayana cewa ba za ta kebance neman tikitin takarar wanda zai gwabza da shugaba Buhari a inuwar ta ba ga yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta gwalashe Sanata Kwankwaso

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta gwalashe Sanata Kwankwaso
Source: Getty Images

KU KARANTA: EFCC ta taso wani Sanatan da yaki komawa APC gaba

Wannan martanin dai na zaman tamkar gwalashewa ne ga tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata dake wakiltar mazabar jihar Kano ta tsakiya a majalisar dattijai game da shawarar da ya bata a farkon makon nan inda ya shawarci jam'iyyar da ta bada tikitin takarar shugaban kasar ta ga wanda yafito daga yankin na Arewa maso yammacin Najeriya.

Legit.ng ta samu cewa wannan matsayar ta jam'iyyar PDP din mai magana da yawun ta ne kuma babban Sakataren yada labarai na jam'iyyar Mista Kola Ologbondiyan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar dauke da sa hannun sa inda ya kuma bayyana cewa su jahohin Arewa baki daya suka ba tikitin.

A wani labarin kuma, Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata a halin yanzu dake wakiltar jihar a majalisar dattijai, Sanata Rabi'u Musa Kwankwanso ya bayyana kalaman Gwamna Ganduje na cewar ba zai iya shiga Kano ba a matsayin abun dariya.

Sanata Kwankwaso ya yace gwamna Ganduje yaron dan siyasa ne da ba zai iya fitowa yayi siyasa da kafafun sa ba sai ya labe bayan Shugaba Buhari domin yasan bai da magoya baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel