Ta zarce kawai: Kasashen duniya sun amince Shugaba Buhari ya zarce a 2019

Ta zarce kawai: Kasashen duniya sun amince Shugaba Buhari ya zarce a 2019

- Kasashen duniya na marmarin Shugaba Buhari ya maimaita a 2019

- Ministan harkokin wajen Najeriya ne ya bayyana hakan

- Kungiyar Afenifere da jam'iyyar PDP sunce karya ne

Babban ministan harkokin wajen Najeriya kuma mamba a majalisar zartarwar kasar nan Mista Geoffrey Onyeama ya karyata labaran da ya bayyana su a matsayin rade-raden da ke yawo na cewa wai kasashen duniya sun bukaci kar Shugaba Buhari ya zarce a zaben 2019.

Ta zarce kawai: Kasashen duniya sun amince Shugaba Buhari ya zarce a 2019

Ta zarce kawai: Kasashen duniya sun amince Shugaba Buhari ya zarce a 2019

KU KARANTA: Wani Kirista yayiwa musulmai sha-tara ta arziki a Kalaba

Mista Onyeama ya bayyana cewa a maimakon hakan ma, kasashen duniyan da dama sun bayyana sha'awar su ga salon mulkin shugaba Buhari din tare kuma da karfafa masa gwuiwar zarcewa a zaben mai zuwa.

Legit.ng ta samu cewa sai dai wasu al'ummomi da dama basu ji dadin kalaman nasa ba kamar kungiyar rajin kare muradun Yarbawa ta Afenifere, fitaccen dan siyasar nan Junaid Mohammed da ma jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, inda suka ce duk karya ce.

A wani labarin kuma, Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata a halin yanzu dake wakiltar jihar a majalisar dattijai, Sanata Rabi'u Musa Kwankwanso ya bayyana kalaman Gwamna Ganduje na cewar ba zai iya shiga Kano ba a matsayin abun dariya.

Sanata Kwankwaso ya yace gwamna Ganduje yaron dan siyasa ne da ba zai iya fitowa yayi siyasa da kafafun sa ba sai ya labe bayan Shugaba Buhari domin yasan bai da magoya baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel