Wani Faston bogi da ya yiwa budurwa fyade ya fada komar ‘yan sanda

Wani Faston bogi da ya yiwa budurwa fyade ya fada komar ‘yan sanda

- Masu ci da addini kasuwa ta baci, asiri ya tonu

- Hukuma ce tayi aikinta kan wani mai fakewa da sunan addini yana aika-aika

- Amma abin mamaki bayan gurfana gaban alkali ya ce shi bai ma san maganar ba

A ranar Alhamis din nan ne aka gurfanar da wani Faston gangan dan kimanin shekaru 32 a gaban kotun majistire dake Ikeja a jihar Lagos, bisa zarginsa da tirsasawa da kuma yiwa wata mata fyade.

Tun da farko dai kotun majistiren tana zargin Faston mai suna Micheal Akpan mazaunin unguwar Obawole Iju da zargin yin fyade ga budurwar mai shekaru 29.

Dan Sanda mai gabatar da kara Sufeto Raji Akeem ya bayyanawa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne tun ranar 17 ga watan Agusta a gidansa.

Ya kara da cewa mutumin ya bayyanawa matar cewa shi Fasto ne, kuma zai yi mata addu’o’I tare da karanta mata littafinsu mai tsarki wanda hakan zai bata kariya daga shaidanu.

KU KARANTA: An cafke wani mai sukar Shugaban Kasa, Mnangagwa, a 'Kasar Zimbabwe

Ya kuma bukaci da ta sayo kwalba bakwai na man zaitun domin yin amfani da shi, sannan ya umarce ta da ta zo gidansa.

Bayan da ta zo gidan nasa ne sai ya rufe kofa, a nan ya yi mata fyade ta karfin tsiya. Daga nan ne wacce aka yiwa wannan ta'asar ta garzaya ofishin ‘yan sanda, inda ta kai rahoton abin da ya faru.

Dan sandan ya shaida cewa abinda Faston bogin yayi ya saba da sashe na 260 na kundin laifuffuka na jihar Lagos.

A karshe alkalin kotun mai shari’a da Jadesola Adeyemi Ajayi ta bayar da belin wanda ake zargin bayan ya musanta aikata laifin kan kudi Naira 200,000, tare da gabatar da mutane biyu masu wadannan adadin kudin. Sannan kuma kotun ta bukaci ya sake bayar da Naira 20,000 wanda duk yana cikin sharadin belin. Sannan kuma kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Oktoba.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel