Hukumar yan sanda ta musanta rahoton birkice gidan tsohon gwamnan PDP da ya koma APC

Hukumar yan sanda ta musanta rahoton birkice gidan tsohon gwamnan PDP da ya koma APC

Hukumar ‘yan sanda a jihar Akwa Ibom ta musanta rahotannin dake yawo a dandalin sada zumunta cewar wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom dake garin Ikot Ntuen a karamar hukumar Essien Udim.

Hukumar ta kara da cewa rahoton dake zagayawar ba gaskiya bane tare da bukatar jama’a su yi watsi da labarin kamar yadda kakakinta a jihar Akwa Ibom, DSP Odiko MacDon, ya sanar.

Hukumar yan sanda ta musanta rahoton birkice gidan tsohon gwamnan PDP da ya koma APC

Godswill Akpabio

Da take fadin gaskiyar abinda ya faru, hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ne su 6 a kan Babura suka je wani gidan man fetur dake daf da gidan Akpabio a ranar 21 ga watan Agusta da misalign 7:20 na yamma.

DUBA WANNAN: Yadda hawan Daushe na Sallah ya gudana a Kano (Hotuna)

Sai dai ‘yan bindigar, da aka dauka cewar sun zo sayen mai ne, sai suka fito da bindigu tare da fara harbin iska kuma a daidai lokacin Akpabio na ganawa da wasu mutane a gidansa.

Hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewar ba tare da wani bata lokaci ba jami’anta suka iso wurin domin fatattakar ‘yan fashin, hakan ne ya saka jama’a yada labarin cewar ‘yan sanda sun birkice gida tsohon gwamnan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel