An cafke wani mai sukar Shugaban Kasa, Mnangagwa, a 'Kasar Zimbabwe

An cafke wani mai sukar Shugaban Kasa, Mnangagwa, a 'Kasar Zimbabwe

Mun samu cewa hukumar 'yan sandan 'Kasar Zimbabwe, ta cafke wani Mutum, Munyaradzi Shoko, bisa laifin cin mutunci da zagin shugaban kasar sa, Emmerson Mnangagwa, a shafin sa na sada zumunta ta Facebook.

Mista Shoko wanda ya shahara da suka gami da caccakar shugaban kasar ya shiga hannun jami'an tsaro kamar yadda lauyoyi suka bayyana ranar yau ta Alhamis.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Shoko ya shiga hannu bayan wani cin mutunci da ya rubuta a shafin sa na sada zumunta da cewa, sunan shugaban kasar kansa yana da alaka da mugunta gami da nasaba ta shaidanu.

Kazalika Shoko ya zargi shugaban kasar da muzgunawa duk masu adawa da gwamnatin sa.

Shugaban 'Kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa

Shugaban 'Kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa

Kakakin Lauyoyin kasar masu kare hakkin dan Adam, Kumbirai Mafunda, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai na jaridar AFP da cewa, jami'an 'yan sandan sun dakume Shoko ne a ranar Larabar da ta gabata.

Mafunda yake cewa, ana zargin Shoko da jagorantar wata Kungiyar ta'addanci tare da aikata miyagun laifuka na gudanar da zanga-zanga ta bayyana adawa ga shugaban kasar bayan kammala zaben a ranar 30 ga watan Yuli.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan zanga-zanga ta yi sanadiyar rayukan mutane shida yayin da dakarun soji suka bude masu wuta.

KARANTA KUMA: Ku haɗa kai domin tabbatar da nasarar Buhari - Sanata Boroffice ya miƙa Ƙoƙon barar sa ga Jiga-Jigan APC

Mnangagwa shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar bayan da tsohon shugaban kasa, Robert Mugabe, yayi murabus wanda kawowa yanzu ake ci gaba da kalubalantar sakamakon wannan zabe a gaban kuliya.

Mugabe ya sauka daga kujerar mulki yayin da dakarun soji suka yi kokarin juyin mulki a watan Nuwamba na shekarar 2017 da ta gabata, bayan ya shafe tsawon kimanin shekaru 40 yana jagorantar kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel