Buhari zai lashe zaben 2019 cikin sauki – Lai Mohammed

Buhari zai lashe zaben 2019 cikin sauki – Lai Mohammed

- Ministan labarai ya bukaci yan Najeriya da suyi taka tsantsan wajen zaben wadanda za su kara tagayyarar da arzikin kasar

- Ya shawarci al'umman kasar da su jajirce domin ganin basu zabi wadanda zasu warware tufkar da wannan gwamnati tayi ba

- Lai Mohammed ya kuma godema yan Najeriya kan irin gudunmawar da suke ba gwamnatin shugaba Buhari da APC

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya yi kira ga al’umman Najeriya da su guje wa zaben wadanda za su dawo kan mulki a kasar nan domin su wawushe dan abin da ya rage ba daga baitul malin kasar.

Minstan yayi wannan kira ne a ranar babban Sallah, a cikin sakon Sallah da ya yi wa jama’a a mahaifarsa ta Oro da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Ya ce: “Shekarar 2019 ita ce shekarar da ‘yan Najeriya za su zabawa kan su mafita.

Buhari zai lashe zaben 2019 cikin sauki – Lai Mohammed

Buhari zai lashe zaben 2019 cikin sauki – Lai Mohammed

Ya kara da cewa ya zama wajibi ‘yan Najeriya su jajirce kada su bari wasu su sake lababowa su warware tubkar igiyar da wannan gwamnati ta daure tattalin arziki, ta hana shi komawa baya ba.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Hakika: Kungiyoyin fafutuka sun yi a gargadi kan yawaitar yan Hakika

Lai ya ce ya tabbatar cewa ganin irin goyon bayan da ake nuna wa Buhari a kasar nan, to zaben 2019 zai zama tamkar wasan yara a wajen Buhari da kuma jam’iyya mai mulki, APC.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, yace akwai bukatar Shugaban kasa mai jajircewa da mayar da hankali akan aiki kamar Muhammadu Buhari ya sake kera tattalin arzikin kasar.

Yace barayin gwamnati sun cinye baitul malin Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel