Ku haɗa kai domin tabbatar da nasarar Buhari - Sanata Boroffice ya miƙa Ƙoƙon barar sa ga Jiga-Jigan APC

Ku haɗa kai domin tabbatar da nasarar Buhari - Sanata Boroffice ya miƙa Ƙoƙon barar sa ga Jiga-Jigan APC

Mun samu cewa, Sanata Mai wakilcin Mazabar Jihar Ondo ta Arewa a Majalisar Dattawa, Ajayi Boroffice, ya yi kira ga shugabannin da mambobin jam'iyyar APC reshen jihar sa kan hadin kai da zaman lafiya yayin da zaben 2019 ke gabatowa.

Sanatan yake cewa, sai an tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a jam'iyyar kana shugaban kasa Muhammadu Buhari zai samu nasara ta cimma burin sa a zaben shugaban kasa.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Sanatan ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da sanadin kakakin sa, Mista Kayode Fakuyi, da ya bayyana a babban birnin Jihar na Akure yayin bikin babbar Sallah a ranar Talatar da ta gabata.

Ku haɗa kai domin tabbatar da nasarar Buhari - Sanata Boroffice ya miƙa Ƙoƙon barar sa ga Jiga-Jigan APC

Ku haɗa kai domin tabbatar da nasarar Buhari - Sanata Boroffice ya miƙa Ƙoƙon barar sa ga Jiga-Jigan APC

Yake cewa, "a yayin da ake cikin wannan lokaci na murna ta babbar Sallah, ya na kuma miƙa ƙoƙon barar sa ga dukkanin mambobin jam'iyyar APC reshen jihar Ondo, akan su hada kai domin tabbatar da nasarar shugaban kasa Buhari da kuma sauran 'yan takara na jam'iyyar a zaben 2019."

KARANTA KUMA: 2019: Ganduje ya kwaɗaitar da Mata kan Zaɓen Shugaba Buhari

"Ko shakka babu akwai kalubalai da jam'iyyar reshen jihar ke fuskanta a halin yanzu, a sakamakon fusatuwa da wasu daga cikin jiga-jigan ta, wanda hakan ke barazana ga nasarar ta a babban zaben mai ci gaba da karatowa."

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, akwai muhimmiyar bukata ta fusatattun jam'iyyar aka su hada kai tare da daukan izina dangane da makamanciyar wannan barazana da zamto kalubale ga wasu jam'iyyun siyasa a tarihi kamar yadda Sanata Boroffice ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel