APC ta nisanta kanta daga ranakun da aka wallafa cewa za’a yi zaben fid da gwani

APC ta nisanta kanta daga ranakun da aka wallafa cewa za’a yi zaben fid da gwani

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta bayyana cewa bata saki jadawalin zabukan fid da gwani na takarar gwamna, yan majalisar dokokin kasar da na shugaban kasa ba, kamar yadda aka rahotoi a wani sashi na kafofin watsa labarai.

Mista Yekini Nabena, babban sakataren labarai na jam’iyyar, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta a Abuja yayinda yake mayar da martani akan lamarin.

APC ta nisanta kanta daga ranakun da aka wallafa cewa za’a yi zaben fid da gwani

APC ta nisanta kanta daga ranakun da aka wallafa cewa za’a yi zaben fid da gwani
Source: Depositphotos

"Jam’iyyar bata sanar da jadawalin zabukan fid da gwani ba tukuna,” cewar kakakin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Jam'iiyar APC ta saki jadawalin zabubbuka da taron gangaminta

Ya bayyana jadawalin dake yawo a kafafen yada labarai a matsayin na bogi, cewa jama’a suyi watsi da shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel