Sabuwar rikici ta barke a jam'iyyar PDP a wata jihar Arewa

Sabuwar rikici ta barke a jam'iyyar PDP a wata jihar Arewa

- Rahottani sun bayyana cewa sabon rikici ya barke a jam'iyyar PDP a jihar Kogi tsakanin shugabanin jam'iyyar da tsohon gwamna Ibrahim Idris

- Rikcin ya barke ne saboda tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Idris na yunkurin bawa 'yan uwansa tikitin takaran zabe a jihar

- Daya daga cikin shugabanin jam'iyyar da baya son a fadi sunansa ya ce ba za amince tsohon gwamnan ya mayar da jam'iyyar ta gado ba

Mun samu rahoton cewa rikici ta barke a jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi sakamakon yunkurin babakere da aka ce tsohon gwamnan jihar Ibrahim Idris yake yi a jihar ta hanyar bawa yaransa da hadimansa a tikitin takarar zabe a 2019.

Vanguard ta ruwaito cewa wasu manyan masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP a jihar sunce wannan yunkurin da Alhaji Idris keyi zalunci ne da kokarin ruguje jam'iyyar a jihar.

Rikici ta barke a jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi

Rikici ta barke a jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi

Legit.ng ta gano cewa wani daya daga cikin shugabanin jam'iyyar da baya son a ambaci sunansa ya ce, "Muna sanne da dukkan makircin da Idris ke shiryawa amma ina son in tabbatar maka cewa ba za mu amince ba. Jam'iyyar PDP ba ta gado bane saboda haka ba zai rika juya ta yadda yake so ba.

DUBA WANNAN: APC da INEC na shirya wata makarkashiya a jihar Osun - PDP

"Za muyi iya kokarinmu na ganin cewa bai mayar da jam'iyyar tamkar gadonsa ba a jihar Kogi. Sai dai idan ya yi nasara, zamu tattara namu ya namu mu koma wata jam'iyyar da ta san darajaramu.

"Wani jami'in mu ya sanar damu cewa Alhaji Idris ya yi rantsuwar cewa zai dena bayar da gudunmawar kudade da yake bawa jam'iyyar muddin ba'a amince da mutanen da yake son a bawa takarar zaben ba."

A wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa tsohon gwamnan na jihar Kogi Ibrahim Idris ya zargi gwamna Yahaya Bello da cin amanar mutanen jihar.

Idris ya koka kan yadda jama'a a jihar ke fama da talauci da wahalhalun rayuwa inda yace gwamnatin Yahaya Bello tayi watsi da bukatun mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel