Rage darajar shugabanci zuwa tafiya kadai abun bakin ciki ne – Dankwambo

Rage darajar shugabanci zuwa tafiya kadai abun bakin ciki ne – Dankwambo

Ibrahim Dankwambo, gwamnan jihar Gombe ya mayar da martani ga fadar shugaban kasa kan yadda ta koda batun tafiyar mita 800 da sugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a ranar Talata, 22 ga watan Agusta.

Shugaba Buhari dai yayi tafiyar tsawon mita 800 daga masallacin Eid zuwa gidansa dake Daura, jihar Katsina.

Fadar shugaban kasa, ta hannun Garba Shehu, kakin shugaban kasa ta bayyana tafiyar a matsayin hujjar cewa shugaban kasar na da lafiyar da zai sake neman takara.

Rage darajar shugabanci zuwa tafiya kadai abun bakin ciki ne – Dankwambo

Rage darajar shugabanci zuwa tafiya kadai abun bakin ciki ne – Dankwambo

KU KARANTA KUMA: Muna bukatar Buhari ya sake kera tattalin aziki – Tinubu

Don haka, a wani lamari da ake kallo a matsayin martani ga furucin Shehu na cewa tafiyar tabbaci ne ga cewa shugaban kasar na da lafiyar ci gaba da mulki, Dankwambo a shafinsa na twitter @HEDankwambo, yace: “Rage darajar shugabanci zuwa tafiya kawai abun bakin ciki ne! 2019, dole mu chanja lamarin.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel