Madalla: Farashin ‘danyan mai ya kara kudi a kasuwa

Madalla: Farashin ‘danyan mai ya kara kudi a kasuwa

- Farashin danyen fetur ya zabura a manyan kasuwanni na Duniya

- Hakan na zuwa ne bayan Kasashe sun fara rage hako danyen mai

Madalla: Farashin ‘danyan mai ya kara kudi a kasuwa

Madalla: Farashin ‘danyan mai ya kara kudi a kasuwa

Labari ya zo gare mu cewa farashin ‘danyan man fetur ya kara kudi a kasuwar Duniya a wannan makon. Hakan na zuwa ne bayan Kasar Amurka ta matsawa Kasar Iran lamba a Duniya. Hakan zai taimakawa tattalin arzikin Najeriya.

Takunkumin da aka makawa Iran ne ya sa man ya tashi har zuwa sama da Dala $74 a kan kowane ganga guda. Dole ta sa kasashen Duniya su ka rage man da su ke hakowa a kowace rana. Sai dai kuma Dalar Amurka ta karye a yanzu.

KU KARANTA: Saudi ta kama Malamin da ya haramta cakuduwar mata da maza

Reuters ta rahoto cewa ana saida man Brent a kasuwa ne a kan Dala 74.19 yayin da man Amurka ya koma Dala 67.12. Rabon da man fetur din yayi wannan tsadar a kasuwannin Duniya dai an yi kwana biyu inji masana tattalin arziki.

A tsakiyar shekarar nan ne ma dai Kasar Saudi Arabia ta rage yawan man da ta take hakowa a kullum. Jama’a dai duk sun yi tunani Saudiyya za ta kara yawon man da ta ke tacewa a duk rana kurum sai aka ji labari ya sha ban-bam.

Kwanaki kun ji labari cewa a a gina wani matatar man fetur a cikin Jihar Katsina. Ana dai sai rai matatar za ta dauki mutum da dama aiki. ‘Yan kasuwa su ka zo da wannan tsari a Arewacin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel