Shekaru 3 sun yi kadan wajen gyaran kasar nan - Tinubu

Shekaru 3 sun yi kadan wajen gyaran kasar nan - Tinubu

- Yawan sukar da ake yiwa gwamnatin jam'iyyar APC ya sanya jagoranta na kasa bukatar ayi musu uzuri

- A cewarsa, barnar da aka yiwa kasar nan ba zata gyaru cikin shekaru uku ba

- Don haka suna da bukatar a sake zabar gwamnatin Buhari a karo na biyu

Jagoran jam'iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa shekaru uku sun yi kadan wajen dawo da kasar nan cikin hayyacinta.

Shekaru 3 sun yi kadan wajen gyaran kasar nan - Tinubu

Shekaru 3 sun yi kadan wajen gyaran kasar nan - Tinubu

Jagoran yayi wannan jawabi ne, a lokacin bikin Sallah babba ranar Alhamis a jihar Legas, sannan ya kara da cewa duk da irin satar kudaden kasa da gwamnatin baya tayi, shugaba Buhari yana cigaba da kokari wajen dawo da martabar kasar nan.

Ya ce "Yan Najeriya sun fara aiki da Dimukuradiyya kuma zasu mori Dimukuradiyya a wannan gwamnati. Muna bukatar shugaba Buhari ya cigaba da mulki domin dawo da kasar nan cikin hayyacinta sannu a hankali, don haka bama bukatar kawo wani nakaso a kasar nan".

KU KARANTA: Hankalinmu ya karkata ne wajen fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci - Osinbajo

"Mun cinye komai, don haka bamu da wani abinda zamu gada ko mu kalla, shi yasa muke maganar barayin gwamnati, amma a sannu komai zai dawo daidai idan aka yi hakuri".

"Shekaru uku sun yi kadan ace an dawo da kasar nan yadda ya kamata. Muna da kyakykyawan zato cewa gwamnatin nan zata yi abin muzo mu gani".

"Tattalin arziki da cigaban matasa shi ne kashin bayan cigaban kowacce kasa, kuma muna yin iya bakin kokari don ganin hakan ta tabbata, duk da cewa abu ne mai wahala ga talakawa".

Jagoran jam’iyyar ya kara da cewa yana matukar alfahari cewa duk wani cigaba da jihar Legas ta samu ta samu ne a lokacin da yake gwamnan jihar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel