Da duminsa: Mutane 3 sun kone kurmus sakamakon wata mummunan hatsarin mota

Da duminsa: Mutane 3 sun kone kurmus sakamakon wata mummunan hatsarin mota

Rahotan da muka samu daga Daily Trust ya ce mutane uku ne suka kone kurmus sannan wasu guda biyar suka sami munnan raunuka sakamakon wata hadarin mota da ta faru a titin Zariagi zuwa Lokaja dake jihar Kogi a safiyar yau Alhamis.

Jami'in wayar da kan mutane na hukumar kiyaye haddura na kasa (FRSC), Mr Bisi Kazeem, ya tabbatar da afkuwar hatsarin inda ya kara da cewa hatsarin ya faru ne a sanyin safiyar yau Alhamsi.

Yanzu-yanzu: Mutane uku sun kone kurmus a Kogi

Yanzu-yanzu: Mutane uku sun kone kurmus a Kogi

Ya yi bayyanin cewa motocci uku ne hatsarin ya ritsa dasu ciki har da wata Toyota Carina da A kori-kura kirar Scania da kuma Tanka guda daya, ya kuma ce mutane tara ne hatsarin ya ritsa da su.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Kazeem ya ce mutum daya da ya tsira da lafiyarsa cikin hatsarin ya ce gudu na fitar hankali da direbobin keyi ya janyo hatsari.

"Wadanda suka rasu sun kone kurmus tare da motoccin yayin da wadanda suka sami rauni suna Asibitin Tarayya da ke Lokoja inda likitoci ke basu kulawa ta musamman."

Ya cigaba da cewa jami'an FRSC da suka iso wajen da hatsarin ya faru sun fara ayyukan kawar da motoccin da sukayi hatsarin daga titin.

Titin Okene-Lokoja-Abuja na daya daga cikin manyan tituna masu hatsari sosai a Najeriya kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel