2019: Ganduje ya kwaɗaitar da Mata kan Zaɓen Shugaba Buhari

2019: Ganduje ya kwaɗaitar da Mata kan Zaɓen Shugaba Buhari

A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kwaɗaitar da Mata kan zaɓen dan takara na gari musamman shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma kansa a zaben 2019.

Ganduje ya bayyana hakan ne a fadar gwamnatin sa yayin bayar da tallafin jari na N30, 000 ga kimanin Mata 6, 600 aka tsakuro cikin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar a ranar Talatar da ta gabata.

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da kudade ga Matan domin su zamto tallafi na gudunmuwa ga kananan sana'o'i da suke gudanarwa kamar yadda Gwamnan ya bayyana.

2019: Ganduje ya kwaɗaitar da Mata kan Zaɓen Shugaba Buhari

2019: Ganduje ya kwaɗaitar da Mata kan Zaɓen Shugaba Buhari

A kalaman Gwamnan ga Matan, "mun yanke shawarar bayar da agaji ga a gare ku domin ƙafarfawa sana'o'in ku ta dogaro da kai da hakan zai taka rawar gani wajen taimakawa 'yan uwa da makusantan ku."

KARANTA KUMA: 2019: Neman Shugabanci ya janyo Rikici tsakanin Mambobin APC a Majalisar Wakilai

Gwamna Ganduje ya kuma bayar da tabbacin cewa, gwamnatin sa za ta ci gaba da dabbaka wannan shiri na bayar da tallafi ga Mata domin dogaro da kai wajen gudanar da sana'o'in su.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan goma ta arziki na daya daga cikin alkawurra da gwamnatin Ganduje da kuma jam'iyyar sa ta APC ta kudirta yayin yakin ta na neman zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel