Dubun wasu barayi ta cika bayan satar na'urar lantarki mallakin MTN

Dubun wasu barayi ta cika bayan satar na'urar lantarki mallakin MTN

- An cafke mutane 3 da satar na'urorin sarrafa wutar lantarki daga hasken rana da kudinsu yakai Miliyan 14.

- Jami'an sa kai na garin Onigbongbo ne suka kama su, daga bisani suka mikasu ga yan sanda.

- Rundunar yan sanda ta tura barayin ga hukumar tsaro ta FSARS don ci gaba da bincike.

Rundunar yan sanda ta jihar Ogun ta samu nasarar cafke wasu mutane guda uku a yankin Atan-Otta dake jihar, bisa laifin satar na'urorin sarrafa wutar lantarki daga hasken rana, da kudinsu yakai Naira Miliyan 14, mallakin kamfanin MTN.

Barayin da aka bayyana sunayen su, sun hada da Kehinde Yahya, 36, Akeem Ademola, 36 and Taofeek Oladele, 36, sun kuma sace na'urorin ne a ranar asabar, 18 ga watan Augusta, sai dai dubunsu ta cika ne lokacin da tawagar jami'an sa kai ta Onigbongbo suka yi ram da su.

Dubun wasu barayi ta cika bayan satar na'urar lantarki mallakin MTN

Dubun wasu barayi ta cika bayan satar na'urar lantarki mallakin MTN

Lamarin ya auku da misalin karfe 12:30 na daren ranar ta asabar, inda jami'an suka kirawo jami'in lardi na rundunar yan sanda dake yankin, SP Abiodun Salau.

KARANTA WANNAN: Jami'ar Obafemi Awolowo ta kori dalibai 6 'yan kungiyar asiri

SP Salau, ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka cafke mutanen uku, ya yin da wasu da ke da hannu a satar suka tsere a wannan dare.

A wata sanarwa daga hannun jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda ta jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce an gano na'urorin guda 12 tare da mota kirar Volkswagen, wacce aka fi sani da Dambo, mai shaidar LND 10 XE,

Ya kuma kara bayyana cewa kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Ahmed Iliyasu, ya bada umurnin gaggawa na tura barayin zuwa ga hukumar FSARS don ci gaba da bincike tare da umarnin ci gaba da nemo sauran barayin da suka tsere.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel