Kuma dai! Atiku ya sake caccakan Buhari da sassafe

Kuma dai! Atiku ya sake caccakan Buhari da sassafe

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takaran kujeran shugaban kasa a 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya sake sukan shugaba Muhammadu Buhari, da sassafen nan kan wasu yan bautan kasa da ya taimakawa a Daura ranar Sallah.

Shugaba Muhammadu Buhari tafi mahaifarsa, Daura, domin bikin babbar Sallah da aka yi ranan Talata, 21 ga watan Agusta, 2018. A yayin tarbar baki da yakeyi a Daura, yan bautan kasa sun kai masa ziyarar yawon Sallah a gidansa.

A wannan ziyara ne shugaba Buhari yayi alkawarin dauka nauyin kudin jinyan wani makahon mai bautan. Wannan abu ya faranta musu rai kuma jama’a sun yaba.

Daga cikin wadanda suka yaba sune Atiku Abubakar amma ya hada da suka inda ya kalubalanci Buhari kan wannan taimako da yayi. Atiku yace da Buhari ya yi amfani da kudin jinya a Landan da yake bannatarwa kan karfafa kiwon lafiya a asibitocin Najeriya, da bai bukaci biyan kudin jinyan matasan ba.

KU KARANTA: Zangon mulki falle daya mai shekaru 6 ne yafi dacewa da kasar nan – Maitaimakin Bukola Saraki

A jawabinsa da ya saki da safen nan yace: “Na yabawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan biyan kudin asibitin masu bautan kasa makaho ana saura watanni biyar da zaben 2019, amma ina tunatar da shi cewa da ya sanya kudin jama’an a yake kashewa kan zuwa jinya Landan kan asibitocin kasa, da bai bukaci yin hakan ba.”

Wannan abu ya biyo bayan jawabin da Atiku ya saki jiya kan labain cewa shugaba Buhari ya yi tattaki kimanin mita 800 daga masallacin Idi zuwa gidansa ranar Sallah.

Atiku ya ce shi yana gudun sama da haka amma bai alfahari da shi kamar yadda fadar shugaban kasa ke alfahari da hakan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel