APC da INEC na shirya wata makarkashiya a jihar Osun - PDP

APC da INEC na shirya wata makarkashiya a jihar Osun - PDP

Jam'iyyar PDP tayi zargin cewa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kammala shirye-shiryen bawa jam'iyyar APC dukkan katunan zaben da mutane basu karba ba domin jam'iyyar tayi amfani da su wajen samun nasara a zaben gwamna da za'a gudanar ranar 22 ga watan Satumba a jihar Osun.

Wannan zargin ya fito ne daga bakin Sakataren yada labarai na jam'iyyar, Diran Odeyemi a wata sako ta ya fitar a jiya Laraba.

Ya yi kira ga hukumomin tsaro su sanya idanu a kan manya-manyan jami'an INEC da shugabanin jam'iyyar APC a jihar domin hana afkuwar lamarin.

PDP tayi ikirarin INEC zata bawa APC katunan zaben da mutane basu karba ba

PDP tayi ikirarin INEC zata bawa APC katunan zaben da mutane basu karba ba

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Odeyemi ya yi ikirarin cewa wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC da bai san ko su wanene ba sunyi yarjejeniya da wasu jami'an INEC domin a basu katinan zaben da mutane basu karba daga hannun INEC ba.

Odeyemi ya ce, "Jam'iyyar APC ta fitar da dan takara maras farin jini, Gboyega Oyetola, hakan yasa jam'iyyar ke kokarin ganin ya yi nasara a zaben ta dukkan hali."

Ya kara da cewa wasu mutane da ake kyautata zaton masu yiwa APC aiki ne sun shiga kauyukan da PDP ke da farin jini suna sayen katinan zaben mutane saboda su ragewa jam'iyyar PDP kuri'u idan zaben ya zo.

Sai dai duk da hakan, Odeyemi ya ce babu wata irin dabara ko makarkashiya da APC za tayi da zai hana ta shan kaye a zaben.

Odeyemi ya shawarci 'yan jam'iyyar APC a jihar su shirya shan kaye saboda duk irin yadda suka nemi murde zaben, dan takarar da jama'a ke kauna ne zai lashe zaben.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel