Dalilin da yasa Saraki ke tsoron dawowa zaman majalisa - APC

Dalilin da yasa Saraki ke tsoron dawowa zaman majalisa - APC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta ce shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki yaki dawowa zaman majalisar dokokin kasar saboda yana tsoron kada a tsige shi.

Mukaddashin sakataren jam’iyyar APC, Mista Yekini Nabena yace sanatan na sane da cewa jam’iyyar nada kaso biyu cikin uku na masu rinjaye da ake bukata don tsige shi.

Nabena yace Saraki na siyan lokaci ne yana tunanin cewa jam’iyyar zata sasanta das hi, inda ya shawarci shugaban majalisar dattawan da ya dawo zaman majalisar dokoki saboda burin kasar.

Dalilin da yasa Saraki ke tsoron dawowa zaman majalisa - APC

Dalilin da yasa Saraki ke tsoron dawowa zaman majalisa - APC

Da aka tambaye shi ko APC na nan akan bakarta na cewa a dawo zaman majalisa domin duba kasafin kudin hukumar zabe mai zaman kanta wanda shugaban kasa ya gabatar da sauran lamura da shugaban jam’iyyar ya tayar, yace “kwarai, saboda hakan ce mafi kyau ga kasar da al’umman kasar idan majalisar dokokin ta dawo. Kasafin kudin abune da zai shafi kowa. Don haka ba wai son rai bane. Kasafin kudi na kasa ne. Dukkanin mun san cewalamarin INEC na tsaye har yanzu, tsaro da tsauran lamarin tattalin arziki na da muhimmanci.

KU KARANTA KUMA: Za mu yi irin abin da Hitler yayi a yakin Duniya a Akwa-Ibom a 2019 – Akpabio

“Don haka har yanzu muna kan bakarmu na cewa shugaban majalisar dattawa ya dawo zaman majalisa. Tsoronsa guda – yana tsoro saboda yasan cewa adadin na nan. Tsoronsa kenan. Amma yana siyan lokaci ne. Duk abunda yake yi yana siyan lokci ne don a sasanta da shi a wannan lokacin.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel