Ba’a rabu da bukar ba: Sojoji sun ragargaji yan bindiga daga Zamfara sun koma Katsina

Ba’a rabu da bukar ba: Sojoji sun ragargaji yan bindiga daga Zamfara sun koma Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya nemi al’ummar jihar Katsina dasu tabbata sun fallasa duk wasu yan bindiga da suka dawo jihar a sakamakon gudun hijirar da yan bindigan Zamfara suke yi zuwa Katsina, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Masari ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 22 ga watan Agusta a yayin da Sarkin Katsina, mai martaba Abdulmuminu Kabir Usman ya kai masa ziyara a fadar gwamnatin jihar Katsina.

KU KARANTA: Yadda yan bindiga suka halaka Sojoji da Dansanda a jihar Ribas

“Ka san Sojoji sun kaddamar da hare hare akan yan bindigan dake jihar Zamfara, don haka wasu daga cikinsu sun fara dawowan dajin Rugu dake Katsina, suna satar shanu, kuma suna garkuwa da mutane, don haka nek kira ga jama’a dasu fallasasu a duk inda suka shiga.” Inji shi.

Ba’a rabu da bukar ba: Sojoji sun ragargaji yan bindiga daga Zamfara sun koma Katsina

Masari

Hakazalika Masari yayi kira ga jama’a dasu tabbata sun yi rajistan katin zabe domin su samu damar kada zabe a zabukan gama gari na shekarar 2019. Daga karshe yayi kira ga iyaye da su kula da yaransu don kauce ma shiga hannun miyagun yan siyasa da zasu yi amfani dasu don tayar da hankula a yayin zaben.

A nasa jawabin, mai martaba Sarki yayi kira ga jama’a dasu tabbatar sun taftace gidajensu don kauce ma barkewar annoban cututtuka daban daban a jihar, haka zalika ya bayyana damuwarsa ga yaduwar kayan shaye shaye da maye a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel