Ban yi na’am da ra’ayin Osinbajo a kan batun rikicin NFF ba – Dalung

Ban yi na’am da ra’ayin Osinbajo a kan batun rikicin NFF ba – Dalung

Yayin da ake cigaba da rikici a Hukumar NFF, Ministan wasannin Najeriya Solomon Dalung ya fitar da wani jawabi wanda ya sha ban-ban da jawabin da Gwamnatin Najeriya tayi kwanaki game da sabanin.

Ban yi na’am da ra’ayin Osinbajo a kan batun rikicin NFF ba – Dalung

Solomon Dalung ya nemi Gwamnati ta bi umarnin Kotu kan rikicin Pinnick da Giwa

A lokacin da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ke rike da kasar nan, Gwamnatin Najeriya ta fitar da matsayar ta game da sa-in-sar da ake yi a Hukumar kwallon kafa na Najeriya watau NFF inda ta tabbatar da shugabancin Amaju Pinnick.

Sai dai Ministan wasannin kasar ya bayyana cewa ba za a bar batun ya wuce haka nan ba inda ya kawo maganar lokacin da aka cire Anthony Kojo Williams daga ofis shekaru kusan 20 da su ka wuce. Ministan yace dole a bi maganar Kotun Koli na kasar.

KU KARANTA: Osinbajo ya bayyana abin da ke gaban Gwamnatin Buhari

Solomon Dalung ya nuna cewa bai yi na’am da matakin da Gwamnati ta dauka na tabbatar da Amaju Pinnick a matsayin Shugaban NFF ba inda yace a matsayin sa na Lauya wanda ya san shari’a kuma Ministan Najeriya dole doka tayi aiki.

Yanzu haka dai ana cigaba da kokarin sulhunta rikicin cikin gidan na NFF wanda ya ja ake daf da hana Najeriya buga-kwallo a Duniya. Minista Dalung ya nemi jama’a su kwantar da hankalin su yayin da wasu manya ke kokarin dinke wannan barakar.

Kwanaki Kotun Kolin kasar ta yanke hukunci cewa Amaju Pinnick ya sauka daga mukamin sa domin kuwa ba ta amince da zaben da ya kawo sa ba. Wannan ya sa Hukumar FIFA ke neman dakatar da Najeriya daga buga kwallon kafa a Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel