Okeowo Olasunbomi ya hakura da takarar Shugaban kasa a zaben 2019

Okeowo Olasunbomi ya hakura da takarar Shugaban kasa a zaben 2019

Mun samu labari cewa Okeowo Olasunbomi ya fasa yin takarar Shugaban kasa a zaben 2019 bayan yayi wata baram-barama a wata hira da yayi kwanan nan inda ya soki bakaken mutane a Duniya.

Okeowo Olasunbomi ya hakura da takarar Shugaban kasa a zaben 2019

Okeowo Olasunbomi yayi kato-barar da ta ja ya fasa takara

Subomi Okeowo wanda ya ke da niyyar takara a 2019 ya maida aniyar sa ciki bayan an ga wata hirar sa inda ya bayyana cewa bakaken mutane dakikai ne. Okeowo dai ya kudiri niyyar tsayawa takara a karkashin ADC a 2019.

Kamar yadda mu ka samu labari, an yi wa Okeowo Olasunbomi tambaya ne game da manufofin sa idan har ya samu kafa Gwamnati, buda bakin sa ke da wuya sai yace bakaken mutane ba su da wata fikira ne kere-kere a Duniya.

KU KARANTA: Sanata Wammako ya taimakawa wani mai kwa-kwa da jari

‘Dan takarar ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa Allah yayi mutanen Najeriya bakaken fara don haka ko shekara nawa za ayi, mutumin Najeriya ba zai iya kera komai a Duniya ba. Okeowo yace dole sai dai Najeriya ta zama ci-ma-zaune.

Wannan Bawan Allah yayi kokarin fayyace bayanin na sa, sai dai tuni hirar ta sa tayi masa barna. Hakan ta sa dai dole ya yafe maganar tsayawar sa takaraa zabe mai zuwa. Kwanaki dai Shugaba Buhari ya kira Matasan kasar malalata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel