Komai yana da rana: Yadda fitsarin shanu zai samar ma Najeriya dala miliyan 600

Komai yana da rana: Yadda fitsarin shanu zai samar ma Najeriya dala miliyan 600

Ilimi kogi inji masu iya magana, hakan ta tabbata a yayin da Najeriya ke kusantar fara amfani da fitsarin shanu wajen yin tattalin arzikin man fetirin kasar, kamar yadda wani Farfesa ya bayyana, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Farfesa Chuma Okoro ne ya bayyana haka a yayin wan taro na masu ruwa da tsaki a harkar kasuwancin man fetir, inda yace a wani bincike da ya gudanar ya nuna cewa fitsarin shanu zai iya magance wata babbar matsala da ake fuskanta a wannan harka.

KU KARANTA: Yadda yan bindiga suka halaka Sojoji da Dansanda a jihar Ribas

Farfesan yace wannan matsala da ake fama da ita itace ta tsatsar bututun man fetir, wanda hakan ke yin sanadin fashewar bututun wanda kuma ke janyo asarar main a miliyoyin daloli, amma yace bincike ya tabbatar da cewa fitsarin shanu zai magance wannan matsala.

Komai yana da rana: Yadda fitsarin shanu zai samar ma Najeriya dala miliyan 600

Bututun mai

Bugu da kari Okoro yace idan aka yi amfani da wannan kimiyyar, fitsarin shanu zai samar na Najeriya sama da dala miliyan dari shidda, wanda suke kudaden da ake kashewa a yanzu wajen shawo kan matsalar.

“Babban matsalar da muke fama da ita a yau a harkar man fetir da iskar gas itace ta tsatsar bututun mai, amma yanzu za’a samu sauki, saboda zamu yi amfani da fitsarin shanu don magance wannan matsalar, kuma hakan zai tara mana makudan kudade.

“Haka zalika muna fata idan hasashenmu ya tabbata muna fata kamfanonin man fetir da iskar gas zasu samar da wurare kiwon shanu don magance rikicin makiyaya da manoma.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel