Yadda yan bindiga suka halaka Sojoji da Dansanda a jihar Ribas

Yadda yan bindiga suka halaka Sojoji da Dansanda a jihar Ribas

Wasu gungun yan bindiga masu tada kayar baya sun bindige wasu dakarun rundunar mayakan sojan kasa guda biyu a karamar hukumar Abua/Odua na jihar Ribas inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun kai hari ne a wani wuri da ake hakar man fetir a kauyen Ogbemakoku, inda anan ne suka bude wuta, inda suka kashe Sojoji biyu, Dansanda guda daya da kuma wani direba.

KU KARANTA: Dakaraun Sojin Najeriya sun yi ma mayakan Boko Haram kisan kiyashi a wata arangama

Yadda yan bindiga suka halaka Sojoji da Dansanda a jihar Ribas

Dan bindiga

Wasu mazauna yankin sun ce yan manufar yan bindigan shine su yi garkuwa da wani farar fata dake aikin hakan man fetirin, toh amma isarsu ke da wuya sai suka ganshi a tsakiyan jami’an tsaro, anan ne suka bude wuta.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jihar Ribas, Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar lamarin.

A wani labarin kuma, wasu yan bindiga sun bindige wani babban Fasto a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, sa'annan suka yi garkuwa da uwargidarsa, wanda har yanzu ba'a samu labarin sakinta ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel