APC za ta ga wuta-wuta idan ta tayar da kura a majalisa – Sanatocin PDP sunyi gargadi

APC za ta ga wuta-wuta idan ta tayar da kura a majalisa – Sanatocin PDP sunyi gargadi

- Da alamun yan majalisar dattawa zasu dawo bakin aiki

- Wasu sanatocin PDP sun bayyana yadda Saraki ya zamewa APC kaikayin ido

Sanata Isah Misau da Sanata Rafiu Ibrahim, na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), sun yi gagadin cewa jam’iyyar the All Progressives Congress (APC) za ta diba kashinta a hannu idan tay kokarin tayar da hankalinsu a majalisar dattawa idan suka dawo bakin aiki.

Majalisar dattawan sun tafi hutu ranan 24 ga watan Yuli ne kuma zasu daow ranan 25 ga watah Satumba, 2018.

A wata jawabi da suka saki, Sanata Misau da Rafiu, sun tuhumci jam’iyyar APC da sanyawa Saraki idon mujiya tamkar ya zaman musu kaya a wuya

Sunyi kira da jam’iyyar APC ta mayar da hankali kan kalubalen da kasa ke fuskanta.

KU KARANTA: Babu ruwanmu barazanar cire Saraki idan abi yi murabus ba – Miyetti Allah ta nisanta kanta

Suka ce: “Wannan shin karo na farko a tarihin kasar nan da jam’iyya mai ci za ta bar al’amuran cigabanta kuma ta fara bin diddigin mutum daya kacal.”

“Kana wannan shine karo na farko da jam’iyya mai ci ke shirin karkata hankulan yan Najeriya uwa ga cewa duk abinda ya faru a gwamnatinta, laifin mutum daya ne.”

“APC ta maya da dukkan lokaci da ilimin shugabanta, kakakinta, sanatocinta hudu da hadiman shugaban kasa biyu wajen zagin Saraki, kai k ace shi kadai ne dan siyasa a Najeriya yau. Sun zamar da Saraki batun tattaunawa a siyasar Najeriya.”

“Saboda haka muna gargadin jam’iyya APC da cewa zasu ga daidai su a PDP idan sukayi kokarin tayar da kura a majalisar dattawa idan muka dawo hutu.”

Sun dade suna kokarin juya majalisar dattawa ta hanyoyin sace sandar ikon majalisa, dukan ma’aikatan majalisa, kuma amfani da jami’an tsaro, kin rattaba hannu ka dokoki masu muhimmanci, amfani a hukumar yaki da rashawa wajen cin mutuncin mambobin majalisa da shugabanninta.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel