Babu ruwanmu barazanar cire Saraki idan abi yi murabus ba – Miyetti Allah ta nisanta kanta

Babu ruwanmu barazanar cire Saraki idan abi yi murabus ba – Miyetti Allah ta nisanta kanta

-Kungiyar Miyetti Allah ta nisanta kanta da jawabin Gololo

- Ta ce ita ba kungiyar siyasa bace saboda haka babu ruwanta da al'amarin ya siyasa

Shugabancin kungiyar Fulani makiyaya ta kasa wato Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta musanta cewa ta yi barazanar tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, idan bai yi murabus daga kujeransa ba.

A wani jawabin da sakataren kungiyar na kasa, Baba Uthman Ngelzarma, ya saki a yai Laraba, kungiyar ta nisanta kanta da jawabin da aka jinginawa wani mambobin kungiyar na jihar Benue, Garus Gololo, wanda yayi magana a wani hira cewa kungiyar za ta tsoge Saraki idan bai yi murabus ba.

KU KARANTA: Cikin shekaru 3 an kai kararrakin aure miliyan N3.5m a wata jiha a Najeriya

Legit.ng ta kawo muku rahoton ceewa shugaban kungiyar Miyetti Allah mna jihar Benue, Alhaji Garus Gololo, ya yi gargadi a hira da ya gabatar a garin Makurdi ranan Talata, 21 ga watan Agusta, 2018.

Gololo ya yi barazanar cewa sun gaji da yadda Saraki ke gudanar da shugabancin majalisar dokokin tarayya. A matsayinsu na kungiya suna son shugaban majalisan da ai girmama fadar shugaban kasa da bangaren shari’a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel