Gwamnatin Buhari ta dukufa wajen gyara barnar da gwamnatin baya ta yi - Lai Mohammed

Gwamnatin Buhari ta dukufa wajen gyara barnar da gwamnatin baya ta yi - Lai Mohammed

- An roki majami'u da su rinka yada manufofi da ayyukan gwamnati mai ci

- An bayyana bukatar wayar da kan jama'a dangane da rikicin manoma da makiyaya

- Gwamnatin tarayya ta gyara barnar da gwamnatin baya ta shafe shekaru 20 tana tafkawa

Gwamnatin tarayya ta roki majami'u da sauran kungiyoyin addinai da su kasance masu yada ayyuka da nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu a cikin shekaru uku.

Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya yi wannan rokon a mahaifarsa dake Oro, kusa da Ilorin, jihar Kwara, lokacin da ya ziyarci babban malamin addinin kirista na majami'ar "St Andrews Catholic", Rev. Fr. Joseph Awoyale.

Ya kuma bukaci majami'u da su yi amfani da wuraren ibadarsu wajen wayar da kan mabiyansu akan labarin kanzon kuregen da ake yadawa na cewar banbancin addini da yare ne suka haddasa rikicin manoma da makiyaya.

Mohammed ya ce rikicin baida wata alaka da banbancin addini ko yare, illa dai rikici ne akan gonaki, iyakoki, da sauran albarkatun kasa.

KU KARANTA WANNAN: Duk da irin tarin matsalolin da kasar ke fuskanta, Buhari ya cancanci a zabe shi 2019

Dangane da nasarorin da gwamnati mai ci a yanzu ta samu, ministan ya ce: "Ba tare da jin shakkar fadar komai ba, babu wata gwamnati da aka taba yi a tarihin kasar nan da ta samu irin wadannan nasarori cikin kankanin lokaci"

“To sai dai, abokan hamayyarmu sun gaza sukarmu akan samar da ayyukan raya kasa, sun koma yada labaran karya don dusashe tauraruwar gwamnati da nufin daga darajarsu.

"Haka zalika, gwamnonin da suka gaza yiwa jama'ar su aiki kan dora laifin kacokan ga gwamnatin tarayya".

Ministan ya bayyana cewa gwamnati na iya bakin kokarinta na gyara barnar da gwamnatin baya tayi na tsawon shekaru 20.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel