PDP ce zata samar da shugaban kasa na gaba - Saraki

PDP ce zata samar da shugaban kasa na gaba - Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi taron sada aminci tsakanin sabbi da tsoffin mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kwara.

Saraki ya bayyana cewa yana da yakinin jam’iyyar ce zata lashe zabuka gaba daya sannan kuma cewa ita ce zata samar da sabon shugaban kasar Najeriya.

Da yake jawabi ga tawagar sabbi da tsoffin yan jam’iyyar shugaban majalisar dattawan yace makomarsu anan gaba zata fin a baya inda yayi alkawarin wanzar da aminci tsakanin bangarorin biyu na jam’iyyar.

PDP ce zata samar da shugaban kasa na gaba - Saraki

PDP ce zata samar da shugaban kasa na gaba - Saraki
Source: Depositphotos

Saraki wanda yace bashi da zabin dantakara a jihar, yace duk dan takarar da yafi shahara da suna, kuma mutane suka nuna shi suke so, toh shima wannan dantakar zai so.

A halin da ake iki, a baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar yakin neman zaben Buhari (BCO) ta bayyana shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da sauransu a matsayin manyan kalubale ga damokradiyya.

KU KARANTA KUMA: Amosun, Lalong da sauransu sun ziyarci Buhari a Daura (hotuna)

Kungiyar ta kuma bayyana su a matsayin kango da babu abunda suka sani sai ihu batre da karfin da zasu iya jerawa da martaba ko farin jinin Buhari ba.

Kungiyar tayi wannan ikirari ne ta jagoranta, Alhaji Danladi Pasali a wata hira da manema labarai a ranar Laraba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel