Cikin shekaru 3 an kai kararrakin aure miliyan N3.5m a wata jiha a Najeriya

Cikin shekaru 3 an kai kararrakin aure miliyan N3.5m a wata jiha a Najeriya

- Matsaltsalun cikin gida na yau da gobe sun yi tsiri saboda yawa

- A jihar Delta kawai cikin shekaru uku, an samu korafin zamantakewar aure kusan miliyan hudu

- Sai dai mahunkuntan jihar sunyi namijin kokari wajen sasanta da yawa daga ciki

A kalla an karbi kararrakin dake da nasaba da aure guda dubu 3,500,000.00 da suka hada; da tauye hakki da cin zarafi a jihar Delta cikin shekaru uku.

A cikin wadannan adadi an samu nasarar sulhunta guda 3,200,000.00, bisa taimakon ma’aikatar harkokin mata da cigaban al’umma ta jihar. A cewar kwamishiniyar ma'aikatar.

Cikin shekaru 3 an kai kararrakin aure miliyan N3.5m a wata jiha a Najeriya

Cikin shekaru 3 an kai kararrakin aure miliyan N3.5m a wata jiha a Najeriya

Kwamishiniyar Rabaran Omatsola Williams ce ta bayyana hakan yayin da take shaidawa manema labarai a garin Asaba.

Ta kara da cewa ma’aikatar ta kuma cimma daidaita aurarrakin da suke cikin tanga-tangal da yawansu ya kai 1,500,000 ta hanyar shawarwari.

KU KARANTA: EFCC ta bawa wani Sanata goron Sallah ta hanyar maka shi a kotu

A cewarta, sun samu nasarar bayar da ‘ya’ya marayu 136 daga cikin guda 693 da ma’auratan da basu da 'ya'ya suka nema bayan tantancewa.

Rabaran Williams ta kuma shaidawa cewa sun killace mutane har 510 da suke gararamba akan tituna masu rangwamen hankali zuwa gidaje bakwai da gwamnatin jihar ta ware domin duba lafiyarsu, wanda har an sada kashi 70% daga cikinsu da iyalansu.

Sannan ta sanar da cewa gwamnatin jihar ta tallafawa mata 300 da suke dauke da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki a jihar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel