Siyasar 2019: Ni gudun sama da mita 1609 nike yi, ba tafiyan mita 800 – Atiku ya yiwa Buhari Isgili

Siyasar 2019: Ni gudun sama da mita 1609 nike yi, ba tafiyan mita 800 – Atiku ya yiwa Buhari Isgili

- Atiku Abubakar yayiwa Buhari hannunka mai sanda

- Ya caccaki shugaban kasan a kaikaice

Awanni bayan labari ya yadu a kafofin yada labarai cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi tattakin mita 800 daga masallacin Idi zuwa gidansa a Daura, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takaran kujeran shugaban, Atiku Abubakar ya bayyana nisan gudun da yakeyi.

Ya yi wannan magana ta kafar sada ra’ayi da zumunta inda ya daura hoton kansa yana gudu kan na’urar jijjiga jini da masu kudi ke amfani da shi.

Siyasar 2019: Ni gudun mita 1609 nike yi, ba tafiyan mita 800 – Atiku ya yiwa Buhari Isgili

Siyasar 2019: Ni gudun mita 1609 nike yi, ba tafiyan mita 800 – Atiku ya yiwa Buhari Isgili

Ya ce shi ba zai ce a zabesa don tafiyar mita 800 ba, amma saboda yana son yiwa yan Najeriya aiki.

Yace: “Na kan yi gudun sama da mil daya kuma in jijjiga jina, amma gidadanci ne in bukaci yan Najeriya su zabeni saboda haka. Ina son jam’iyyata PDP da yan Najeriya su zabeni saboda aiki ba tafiya ba.”

Wannan raddi ya biyo bayan jawbain mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, inda yace tafiyan mita 800 da shugaba Buhari yayi na nuna cewa yanada lafiyan takaran zaben 2019.

KU KARANTA: Bayan tsanani akwai sauki: Dan jaridar da hukumar DSS ta tsare shekaru 2 ya samu 'yanci

Alhaji Atiku Abubakar ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP domin tsayawan takara kujeran shugaban kasan Najeriya a shekarar 2019.

Yana aya daga cikin yan takaran jam’iyyar PDP 8 da suke neman tikitin jam’iyyar PDP na takarar kujeran a zaben bana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel