Jami'ar Obafemi Awolowo ta kori dalibai 6 'yan kungiyar asiri

Jami'ar Obafemi Awolowo ta kori dalibai 6 'yan kungiyar asiri

- An kori dalibai 6 daga jami'ar Obafemi Awololo

- Binciken da jami'an tsaro sukayi ya tabbatar da cewa daliban suna cikin kungiyar asiri

- Tun farko an zargi dalibai 12 da tursasa wasu dalibai 2 shiga kungiyarsu ta asiri

Jami’ar Obafemi Awolowo, (OAU) da ke Ile Ife, jihar Osun ta kori dalibai shida daga jami’ar, bayan kama su da laifin shiga kungiyoyin asiri.

Daliban da aka kora sune:

• Onyekwusi Praise Chinemerem, mai lambar rijista ASE/2014/218,

• Ojo Abiodun Olamide, mai lambar rijista MCB/2012/149,

• Ude John, mai lambar rijista ASE/2015/362,

• Oladoye Tobi Olakunmi, mai lambar rijista EGL/2014/383,

• Ayeyi Damilola Ayomide, mai lambar rijista EGL/2016/075

• Davis Jesulayomi Olakunle, mai lambar rijista EGL/2014/207.

Jami'ar Obafemi Awolowo ta kori dalibai 6 'yan kungiyar asiri

Jami'ar Obafemi Awolowo ta kori dalibai 6 'yan kungiyar asiri

An kore su ne biyo bayan wani bincike da akayi, a zargin da a ke masu na tursasa wasu daliban jami’ar biyu shiga kungiyarsu ta asiri.

KARANTA WANNAN: Yan Nigeria na cin shinkafar dabbobi da ta lalace

A yayin binciken, an cafke daliban jami’ar guda 12, inda aka mika su ga hukumar ‘yan sanda ta jihar Osun, don ci gaba da bincike kan lamarin.

Bayan kamala binciken ‘yan sanda, an samu tabbacin cewa dalibai shida na cikin kungiyar asiri wanda hakan ya sabawa rantsuwar da sukayi yayin shigarsu makarantar, dama karya wasu dokoki na jami’ar.

Da yake tabbatar da faruwar hakan, magatakardar jami’ar, Magaret Omosule ya ce: “Bayan da jami’an yan sanda suka kamala nasu binciken, an samu tabbacin cewa daga cikin dalibai 12 da aka tsare, akwai dalibai 6 da suka amsa zargin da ake masu na kasancewa cikin kungiyar asiri”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel