Ma’aikacin CBN ne ya roke ni da na kashe shi – Mai laifi

Ma’aikacin CBN ne ya roke ni da na kashe shi – Mai laifi

Rundunar yan sanda a Abuja sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da kashe ma’aikacin babban bankin Najeriya, Michael Iorkohol, mai shekaru 47 wanda iyalansa suka sanar da batansa kafin aka gawarsa a garin Piyako dake Abuja.

An gano masu laifin, Alfred Leonard da Samson Agbo,dauke da agogon hannu, majayi, riga, takalma, katin ATM da kuma katin shaida na mamacin.

Da yake gurfanar da masu laifin tare da wasu mutane 47 a ranar Litinin, kwamishinan yan sandan birnin tarayya, Bala Ciroma, yayi bayanin cewa bincike ya nuna cewa gani na karshe da akayiwa Iorkohol ya kasance tare da Leonard.

Ma’aikacin CBN ne ya roke ni da na kashe shi – Mai laifi

Ma’aikacin CBN ne ya roke ni da na kashe shi – Mai laifi

Sai dai da yake bayanin kasanewarsa a kisan, Leonard yace Iorkohol na karkashin kulawarsa tsawon watanni takwas, inda ya kara da cewa yana da ciwon ciki.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi takawar mita 800, Obasanjo ya buga kwallon kafa, Jonathan ya motsa jiki - Yadda shugabannin Najeriya ke motsa jikinsu (hotuna)

Yace shi ke basa magani inda ya fada masa ewa yan cikin kungiyar asiri sannan ya roke shi da ya kashe shi kuma kada ya sanar da iyalansa.

Yace ya shawarce shi da ya koma kungiyar asirin sannan ya mayar masu duk abunda yake nasu amma yace sun ce zasu kashe shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel