Buhari da tsoffin shugabanni sun gazawa yan Najeriya – Dan takarar shugaban kasa

Buhari da tsoffin shugabanni sun gazawa yan Najeriya – Dan takarar shugaban kasa

Wani dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar National Rescue Movement, Alhaji Usman Ibrahim, ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran tsoffin shugabannin kasar sune suka haddasa matsalolin Najeriya.

Ibrahim wadda ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa a yammacin ranar Litinin yace ya yanke shawarar kaddamar da kudirinsa a jihar Osun domin jiha ce ta daban.

Buhari da tsoffin shugabanni sun gazawa yan Najeriya – Dan takarar shugaban kasa

Buhari da tsoffin shugabanni sun gazawa yan Najeriya – Dan takarar shugaban kasa

A cewarsa, shugabannin Najeriya sun dade suna amfani da tsoffin manufofi wajen tafiyar da kasar a zamanin kimiya.

KU KARANTA KUMA: Ba zan sanya baki a zaben fid da gwani na gwamna ba – Gwamna Shettima

Ibrahim yayi alkawarin cewa zai tabbatar da ingantaccen tsaro na rayuka da dukiyoyin jama’a, zai magance cin hani da rashawa, sannan kuma zai samar da ingantattun tsare-tsare da ake bukata wajen habbaka tattalin arziki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel