Jam'iyar APC ta kaddamar da gagarumin shirin rijistar sabbin mambobi

Jam'iyar APC ta kaddamar da gagarumin shirin rijistar sabbin mambobi

A shirye shiryen da takeyi don fuskantar babban zaben 2019, jam’iya mai mulki ta APC ta samar da sabbin hanyoyin da zasu baiwa masu sha’awar shiga jam’iyar damar yin rijista.

Hukumar gudanarwar jam’iyar ta kasa, ta amince da ci gaba da yin rijista ga wadanda ke da sha’awar shiga jam’iyar a jihohi 36 dake fadin kasar, hadi da babban birnin tarayya Abuja.

“Amincewa da wannan bukatar ya biyo bayan kiraye-kiraye daga al’umar kasar da ke da sha’awar shiga wannan babbar jam’iya tamu, don bada gudunmowarsu wajen samun nasarar kudurorin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari” a cewar kakakin jam’iyar, Yekini Nabena, a Abuja.

KARANTA WANNAN: 2019: Duk da tarin matsalolin Nigeria Buhari ya cancanci a zabe shi

Ya ce akwai shirye shirye da akayi don yin rejista ga masu sha’awar shiga jam’iyar da kuma sabunta rejistar tsoffin mambobi, don samun damar yi masu katin zama ‘yan jam’iyar na din-din-din.

“Don haka muke bukatar daukacin magoya bayanmu da mambobin jam’iyar dasu yi amfani da wannan dama da suka samu”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel