Bayan tsanani akwai sauki: Dan jaridar da hukumar DSS ta tsare shekaru 2 ya samu 'yanci

Bayan tsanani akwai sauki: Dan jaridar da hukumar DSS ta tsare shekaru 2 ya samu 'yanci

- Hukumar DSS ta kama Mr. Abiri a ofishinsa ba tare da ya san laifinsa ba

- Tsawon shekaru biyu ya kwashe a kurkukun hukumar ba tare da yin Magana da kowa ba

- Da taimakon kungiyoyin dake fafutukar kare hakkin d’an Adam ya samu ‘yan cin sa

Wani dan jarida dake aiki a kamfani jarida na Weekly Source, da ke jihar Bayelsa, Mr Jones Abiri, a ranar talata ya samu ‘yancin komawa babban birnin jihar wato Yenagoa, bayan kubutarsa daga hannun jami’an tsaro na farin kaya, DSS.

Mr. Abiri, wanda aka tarbe shi a sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ reshen jihar da kuma shuwagabannin kungiyar ‘Civil Liberties’, yace jami’an DSS sun cafke shi ne a cikin ofishinsa, inda suka tsare shi a wajensu na tsawon kwanaki bakwai, daga bisani suka garzaya da shi Abuja.

Ya ce tsawon shekaru biyu ya shafe a cikin kurkukun karkashin kasa na hukumar tsaro ta DSS ba tare da sun barshi yayi Magana da kowa ba, kazalika ba tare da sun bashi kulawa akan lafiyarsa ba.

Bayan tsanani akwai sauki: Dan jaridar da hukumar DSS ta tsare shekaru 2 ya samu 'yanci

Bayan tsanani akwai sauki: Dan jaridar da hukumar DSS ta tsare shekaru 2 ya samu 'yanci

Abiri, wanda ya kuma samu tarba daga matarsa da ‘yan uwansa, ya ce sanya yakini a ranshi cewa Allah zai kubutar dashi wata rana, ya sa har yake raye zuwa wannan lokaci da ya samu ‘yancinsa.

Dan jaridar yace: “A ranar 21 ga watan Yulin shekara ta 2016 ne aka kamani, ina zaune a cikin ofishina, da misalin karfe 3:23 na rana. Akalla jami’an hukumar DSS 12 ne suka shigo ofishin, suna tafe da takardar basu izini na yin bincike a cikin ofishin.

“Da nayi bincike akan takardar, sai na ga tana dauke da sa hannun wani Majistire mai suna Lucky. Na basu dama don su yi bincike a ofishin. A karshen binciken dai basu gano komai ba. Sai suka sanya min ankwa tare da kwace wayoyina, na’urar kwamfuta da dai sauransu.

“Sun tafi dani zuwa ofishinsu na jiha, a nan na bayar da nawa bayanin, inda suka tsare ni na kwanaki bakwai a Yenagoa, daga bisani suka wuce dani Abuja. Ba su bani wata dama na ganin matata, ‘yayana, ‘yan uwana dama abokai na ba.

“Haka zalika sun hana lauyoyina ganina. Sun ajiye ni a wani kurkuku na karkashin kasa, inda babu koda hasken wutar lantarki balle hasken rana. A bangaren lafiyata ma basu bani damar ganawa da likita ba. Na godewa Allah da yasa kungiyoyin sa kai suka yi ta fafutukar ganin na samu ‘yanci, a yau gani tare da iyalina".

Mr. Abiri ya bayyana cewa hukumar tsaro ta DSS tana tuhumar sa da aikata laifi daya ne, na aika sakon barazana ga kamfanin Agip Nigeria Limited da Shell Petroleum Development Company, da cewar yana bukatar su bashi kudi.

“Sai dai har kullum amsa daya nake basu, cewa ni ban san komai dangane da wannan zargi da ake yi mun ba, bani da wata alaka da wadannan kamfanonin mai” a cewar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel