Yanzu Yanzu: Fusatattun matasa sun cinna wa kotun majistare wuta a Imo

Yanzu Yanzu: Fusatattun matasa sun cinna wa kotun majistare wuta a Imo

An samu rudani a kotun majistare dake Orlu, jihar Imo, yayinda matasa sama da goma sha biyar suka cinna wa ginin kotu wuta.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wuta ta lalata dukkanin takardun kotun kafin a iya kashe ta.

Yanzu Yanzu: Fusatattun matasa sun cinna wa kotun majistare wuta a Imo

Yanzu Yanzu: Fusatattun matasa sun cinna wa kotun majistare wuta a Imo
Source: Depositphotos

Kotun majistare din na a harabar babban kotun Orlu ne. Kakakin yan sandan jihar, Enwerem wadda ya tabbatar da lamarin ga manema labarai ya bayyana cewa lamari ne na sa wuta da gangan.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta caccaki Tambuwal kan cewa da yayi Buhari ya tsufa da shugabanci

Enweren ya bayyana cewa kwamishinan yan sanda, Daduki Galadanchi ya umurci kwamandan yankin da ya sa ofishin Orlu su fara bincike akan lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel