Hankalinmu ya karkata ne wajen fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci - Osinbajo

Hankalinmu ya karkata ne wajen fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci - Osinbajo

- Gwamnatin tarayya ta sake jadda kudirinta na magance kamfar talauci a kasar nan

- Mataimakin shigaban kasa Yemi Osinbajo ne ya sanar da hakan yayin wani taro

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo ya ce gwamnatin tarayya ba ta da wani buri face fitar da Najeriya daga kangin talauci.

Yace dukkan wasu ayyuka da gwamnatinsu ke yi, tana yi ne don ganin ta cimma wannan kuduri nata.

Hankalinmu ya karkata ne wajen fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci - Osinbajo

Hankalinmu ya karkata ne wajen fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci - Osinbajo

Hakan ya fito ne a cikin wani wajabi da babban mai bawa mataimakin shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai Mista Laolu Akande ya fitar a yau labara, yayin wani zaman masu ruwa da tsaki da mataimakin shugaban kasar ya halatar a yankin Bariga/Somolu dake jihar Legas.

Osinbanjo ya ce "Ina so na tabbatar da cewa muna yin duk abinda zai kawo karshen talauci a cikin al'umma".

"Muna da babbar kasa wadda take dauke da sama da mutane miliyan 200, amma zamu tabbatar mun taimakawa duk wanda yake da abin yi, musamman kananan sana’o’i".

"Dalili kuwa idan ka duba gwamnatin da ta gabata zaka ga tafi maida hankali ne a yayin kasafin kufi akan mutanen da suke tsaka-tsaki, masu kamfanunuwa, da sauransu".

"Amma idan aka duba za a ga na kasa su ne suke shan wahala, mu kuma su ne mutanen da muke son taimako, saboda in har na kasa yaji dadi, to komai zai tafi daidai".

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bukaci shuwagabannin hukumomin tsaro na kasa su kara zage damtse

Osinbanjo ya kara da cewa gwamnatinsu tana cigaba da yin duk mai yiwuwa wajen ganin an samar da walwala ga talakan kasar nan.

"Lokacin da muka zo mulki, shugaban kasa ya jadadda cewa dole mu kawo karshen rashin aikin yi, misali mun kawo shirin N-Power wanda ake daukar matasan da suka gama makaranta basu da aikin yi".

"Da farko mun fara daukar matasa guda dubu 200,000, sannan a wannan watan da muje ciki mun sake daukar dubu 300,000.

Ya zuwa yanzu shirin N-power ya dauki adadin matasa guda dubu 500,000 a fadin tarayyar Najeriya, kuma babu wata karamar hukumar da zaka je a fadin kasar nan ba tare da an samu matashin da yake cin moriyar shirin N-power ba" a cewar Osinbanjo.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel