Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai mamaya gidan sanata Akpabio

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai mamaya gidan sanata Akpabio

Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga sun kai mamaya mahaifar sanata Godwill Akpabio a ranar Talata, 21 ga watan Agusta da misalin karfe 7:30 na yamma a jihar Akwa Ibom, inda yake gabatar da taron siyasa jaridar Premium Times ta ruwaito.

Hadimin mista Akpabio a shafukan zumunta, Anietie Ekong ya bayyana hakan a shafin Facebook a daren ranar Talata.

Mista Ekong ya rubuta a shafin zumunta, “yanzu haka: wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba na harbi a Ukana Ikot Ntuen, karamar hukumar Essien Udim, mahaifar tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisa Sanata Godswill Akpabio.

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai mamaya gidan sanata Akpabio

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai mamaya gidan sanata Akpabio

“Jami’an yan sandan yankin Essien Udim da kwamishinan yan sandan jihar Akwa Ibom yayi gaggawan kawo doki.”

KU KARANTA KUMA: Zai dauki Najeriya tsawon shekara 10 kafin ta farfado idan Atiku ya zama shugaban kasa na rana 1 - Okupe

Wasu daga cikin mutanen dake zama kusa da gidan Akpabio a Ukana Ikot Ntuen, Essien Udim, sun bayyana cewa sun lura da motocin yan sanda da yawa da aka ajiye a gaban gidan sanatan da safe, misalin karfe 6:30.

Hadimin nasa yace Sanatan na cikin koshin lafiya a safiyar yau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel