An min tayin kujerar Ekweremadu amma naki amincewa - Sanata Abaribe

An min tayin kujerar Ekweremadu amma naki amincewa - Sanata Abaribe

- Hatsaniyar majalisar tarayya na cigaba da shiga kusufi

- A yunkurin tsige Saraki da mataimakinsa, an yi wa wani Sanata tayin kujerar mataimakin Saraki

Sanata Enyinnaya Abaribe ya bayyana cewa wasu masu ruwa da tsaki sun tunkare shi domin maye gurbin Ike Ekweremadu a matsayin mataimakin shugaban majalisar datijjai.

Idan ba’a manta ba akwai shirye-shiryen da jam'iyyar APC tayi domin tsige Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu.

An min tayin kujerar Ekweremadu amma naki amincewa - Sanata Abaribe

An min tayin kujerar Ekweremadu amma naki amincewa - Sanata Abaribe

Bayan sauya shekar Saraki daga jam'iyyar APC, masu ruwa da tsaki na jam'iyyar suna ganin cewa tunda sune masu rinjaye a majalisar ya kamata ace an tsige Ekweremadu daga kujerarsa.

Sai ga shi Sanata Abaribe ya bayyanawa zauren gwamnonin kudu maso gabas cewa bai shiga majalisa domin neman shugabanci ba, sai dan samarwa da jama'ar da yake wakilta abubuwan cigaba na rayuwa.

Ya ce "Babbar matsalarmu a majalisa shi ne kawo karshen kalubale daga wajen ayyukan rukuni-rukuni".

KU KARANTA: 2019: Duk da tarin Matsalolin Nigeria, Buhari ya cancanci a sake zabarsa -Sanata Sani

Ya kara da cewa, dalili daya da yasa Ekweremadu ya cigaba da zama a matsayin mataimakin shugaban majalisar datijjai, shi ne domin kawo hadin kan sanatocin kudu maso gabas.

"An tunkareni da maganar maye gurbin Ekweremadu amma na sanar da su cewa wannan ba shi ne dalilin da yasa muka zo majalisa ba".

Daga nan ne Sanatan ya kalubalanci gwamnatocin jahohin kasar nan da su nuna jagoranci na gari kafin su kalubalanci gwamnatin tarayya.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel