Fadar shugaban kasa ta caccaki Tambuwal kan cewa da yayi Buhari ya tsufa da shugabanci

Fadar shugaban kasa ta caccaki Tambuwal kan cewa da yayi Buhari ya tsufa da shugabanci

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga ikirarin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal na cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baida isashen lafiyar da zai sake takara karo na biyu.

Tambuwal a makon da ya gabata ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsufa da sake shugabantar Najeriya, duk da kyawawan hallayarsa.

Gwamnan ya bayyana hakan a yayin ziyarar da kaiwa dalibai da matasan Sokoto a makon da ya gabata.

Fadar shugaban kasa ta caccaki Tambuwal kan cewa da yayi Buhari ya tsufa da shugabanci

Fadar shugaban kasa ta caccaki Tambuwal kan cewa da yayi Buhari ya tsufa da shugabanci

Sai dai, Malam Garba Shehu, babban hadimin shugaban kasa a kafafen yada labarai yace takawar da shugaban kasar yayi ya isa martani ga Tambuwal.

KU KARANTA KUMA: Zai dauki Najeriya tsawon shekara 10 kafin ta farfado idan Atiku ya zama shugaban kasa na rana 1 - Okupe

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Buhari ya yi takawar mita 800 daga masallacin Idi zuwa gida a garin Daura.

Bayan nan matasa masu bautar kasa suka ziyarce shi domin yi masa gaisuwar Sallah.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel