Zai dauki Najeriya tsawon shekara 10 kafin ta farfado idan Atiku ya zama shugaban kasa na rana 1 - Okupe

Zai dauki Najeriya tsawon shekara 10 kafin ta farfado idan Atiku ya zama shugaban kasa na rana 1 - Okupe

Wani tsohon hadimin tsoffin shugabannin kasa Goodluck Jonathan da Olusegun Obasanjo, Doyin Okupe yace Najeriya ba zata taba cigaba ba idan har tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi nasara akan kudirinsa na son shugabancin kasa.

Ku tuna cewa Atiku, tsohon jigon jam’iyyar Progressives Congress (APC), ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a shekarar da ta gabata.

Yana daya daga cikin yan takarar kujerar shugaban kasa a babban jam’iyyar adawa a zabe mai zuwa.

Zai dauki Najeriya tsawon shekara 10 kafin ta farfado idan Atiku ya zama shugaban kasa na rana 1 - Okupe

Zai dauki Najeriya tsawon shekara 10 kafin ta farfado idan Atiku ya zama shugaban kasa na rana 1 - Okupe

Don haka, Okupe yace shugabancin Atiku zai kawowa Najeriya koma baya sannan kuma cewa zai dauki ksar tsawon shekara goma kafin ta fita daga wannan hali.

Ya wallafa hakan ne a shafinsa na twitter.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana babba dalilin da ya sanya al'ummar kasar na masu kishi ke muradin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce har bayan 2019.

KU KARANTA KUMA: Oshiomhole ya gana da shugabannin Edo ta Arewa

Gwamnan yake cewa, shawarar da masu kishin kasar nan su yanke na goyon bayan shugaba Buhari har bayan 2019 ba wani abu face tsagwaran neman hakikanin jagoranci na gaskiya gami da adalci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel