Dakarun soji sun cafke wani barawon shanu tare da kwato shanu 49 a Kaduna

Dakarun soji sun cafke wani barawon shanu tare da kwato shanu 49 a Kaduna

- Rundunar soji dake atisayen 'WHIRL Punch' ta cafke wani barawon shanu a Kaduna

- Mataimakin darakta janar na rundunar ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a Kaduna

- Ya ce rundunar ta kuma samu nasar kakkabe wata maboya ta 'yan ta'addan da suka addabi yankin Kaduna zuwa Abuja

Rahotanni na nunancewa, rundunar soji dake karkashin atisayen 'WHIRL Punch' ta samu nasarar cafke wani barawon shanu tare da kwato shanu 49 daga hannunsa a kauyen Gwagwada dake karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.

Mataimakin Daraktan jami'in hulda da jama'a na rundunar, Col. Muhammad Dole, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Kaduna.

Dole ya ce rundunar sojin sun kai sumamen ne bayan da suka samu bayani kan irin ta'addancin da akeyi da kuma bulluwar wasu barayin shanu a kauyen na Gwagwada.

"A sumamen da dakarun suka yi, an cafke wani barawon shanu da kwato shanu 49 daga hannunsa" a cewar Dole.

KARANTA WANNAN: Yadda amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu

Ya kuma bayyana cewa dakarun sojin na (1 Div NA) dake atisayen 'WHIRL PUNCH', sun samu kwararan bayanai daga majiya mai tushe, inda wasu 'yan ta'adda suka maida kauyen Jumu dake karamar hukumar mafakarsu ta yin ta'addanci a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

"Dakarun sun kai sumame wajen, don kwantar da duk wani dan ta'adda dake a yankin"

Sai dai mataimakin daraktan ya ce tuni yan ta'addan suka arce da suka fahimci dakarun zasu kai masu hari.

"Bayan da dakarun sojin suka lalata maboyar, an gano bindiga kirar AK47, da kuma wata bindigar kirar cikin gida" a cewar sa.

Ya baiwa al'uma tabbacin cewa rundunar zata ci gaba da mamaye yankin Kaduna zuwa Abuja da kuma Kaduna zuwa Birnin Gwari, don dakile ta'addancin da akeyi a yankunan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel