Bayan kashe mijinta, an bukaci Naira miliyan N5m domin sako matarsa da akai garkuwa da ita

Bayan kashe mijinta, an bukaci Naira miliyan N5m domin sako matarsa da akai garkuwa da ita

- Masu garkuwa da mutanen da suka kashe mijin wata mata a Coci sun nemi makudan kudade kafin sako ta

- Wanna ke nuna cewa har yanzu da sauran aiki a fanni tsaro a Najeriya

Masu garkuwa da mutane wadanda har yanzu ba’a kai ga gane su ba da suka kashe wani malamin addinin Kirista a jihar Kaduna tare da yin garkuwa da matarsa, sun bukaci a basu Naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa, domin sako matar mamacin.

Bayan kashe mijinta, an bukaci Naira miliyan N5m domin sako matarsa da akai garkuwa da ita

Bayan kashe mijinta, an bukaci Naira miliyan N5m domin sako matarsa da akai garkuwa da ita

Idan za'a iya tunawa dai a ranar Litinin ne masu garkuwa da mutanen suka kai hari kan wata cocin Nasara dake unguwar Guguwa a garin Kadinal, a inda suka kashe malamin Cocin mai suna Rabaren Hosea M Akuchi tare da yin garkuwa da matarsa mai suna Talatu H Akuchi.

Wasu rahotanni sun rawaito cewa masu garkuwa da mutanen sun yi wa Cocin tsinke ne da misalin karfe daya na rana (1:00pm), suka kutsa kai tsaye inda Faston yake sannan suka harbe shi, kana suka yi awon gaba da matarsa.

KU KARANTA: Dakaraun Sojin Najeriya sun yi ma mayakan Boko Haram kisan kiyashi a wata arangama

Wata Majiya ta bayyana cewa masu garkuwar sun kirawo iyalin wannan mata a wayar sadarwa, inda suka bukaci a basu Naira miliyan 5 domin su sako ta.

"Bayan kashe Fasto ba tare da hakkinsa ba, kuma a bukaci wasu makudan kudade domin sakin matarsa, hakika abin akwai takaici da bakin ciki" Majiyar ta bayyana.

A nata bangaren rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kaduna ta bakin kakakin ta DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da faruwa al'amrin, inda ya bayyana cewa jami'an ‘yan sanda suna bakin kokarinsu domin magance matsalar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel