Ko dai Saraki ya yi murabus cikin ruwan sanyi ko mu tursasa shi -Miyetti Allah

Ko dai Saraki ya yi murabus cikin ruwan sanyi ko mu tursasa shi -Miyetti Allah

- Kungiyar Miyetti Allah ta ce zata tursasa Bukola Saraki yin murabus

- Saraki ya jawowa Nigeria matsaloli da dama da suka haddasa durkishewar arzkinta

- Al'uma na neman mutanen da ke son talaka a zuciyarsu, ba irin Saraki ba

Kungiyar Fulani ta "Miyetti Allah Cattle Breeders" ta gargadi shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, da cewar ya yi murabus daga kujerarsa cikin ruwan sanyi ko kuma kungiyar ta tursasashi yin hakan.

Kodinetan kungiyar na kasa a jihar Benue, Alhaji Garus Gololo, shi ne ya yi wannan gargadi a zantawarsa da manema labarai a Makurdi.

Gololo ya ce Saraki ya haddasa matsaloli da dama ga gwamnatin shugaba Muhammad Buhari, wanda ya ce hakan ya kawo nakasu ga tattalin arziki dama ci gaban kasar.

Ko dai Saraki ya yi murabus cikin ruwan sanyi ko mu tursasa shi -Miyetti Allah

Ko dai Saraki ya yi murabus cikin ruwan sanyi ko mu tursasa shi -Miyetti Allah

KARANTA WANNAN: EFCC ta bawa wani Sanata goron Sallah ta hanyar maka shi a kotu

"A dai dai wannan gabar muke kira ga Saraki da yayi murabus, bai can-canci komawa kujerarsa ta shugabancin majalisar dattijai ba, Saraki ya gaza hada kan yan majalisar dokoki wajen yin shugabanci nagari ga bal'uma

"Nigeria na bukatar mutanen da ke son talaka a zuciyar su. Kungiyar Miyetti Allah tana bukatar shugaban da zai jagoranci majalisar dattijai cike da biyayya ga majalisar zartaswa ta kasa dama fannin shari'a, ba irin Saraki ba, wanda kullum burinsa ya kuntatawa Buhari.

"Mu mun gaji da irin shugabancin Saraki, Don haka muke yi masa gargadi, da ya yi murabus cikin ruwan sanyi daga matsayinsam ko mu tursasashi yin hakan", a cewar Gololo, duk da yaki bayyana yadda kungiyar tasu zata iya sauke Saraki.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel