Har anyi Sallah amma Buhari bai biya albashi ba – matasan Musulmai sun koka

Har anyi Sallah amma Buhari bai biya albashi ba – matasan Musulmai sun koka

Wata kungiyar matasa Musulmai sun caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo akan rashin biyan albashn watan Agusta, duk da cewa Sallah ya fado daga karshe karshen watar, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kungiyar, Abdulhamid Adamu ne ya bayyana haka a ranar Sallah a yayin taron manema labaru, inda yace rashin ma’aikatan gwamnatin tarayya ya takura mutane da dama a wannan Sallar.

KU KARANTA: Dakaraun Sojin Najeriya sun yi ma mayakan Boko Haram kisan kiyashi a wata arangama

Abdulhamid yace da ace Buhari da Osinbajo sun daure sun biya ma’aikata albashinsu, da jama’a da dama sun walwala tare da sayan raguna a yayin shagulgulan Sallah.

“Gwamnatin tarayya ta biya albashi ga ma’aikata kafin bikin Kirismeti na shekarar data gabata, wanda hakan ya basu damar yin bikin kirismeti cikin jin dadi, amma sai ga shi a yanzu an hana Musulmai albashinsu, hakan ba zai haifar da Da mai ido ba musamman yadda ake tunkarar zabukan 2019.” Inji shi.

Daga karshe kungiyar ta jinjina tare da yaba ma gwamnonin jihohin da suka biya albashin ma’aikata na watan Agusta don samun saukin gudanar da bukukun Sallah cin jin farin ciki da kwanciyar hankali.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel